Tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana talauci a matsayin babbar barazana ga zaman lafiyar kasa da mutuncin dan Adam.

Atiku ya bayyana hakan ne a cikin wata wallafa da ya fitar a ranar Asabar, domin tunawa da ranar kawar da fatara ta duniya.
Alhaji Atiku ya bayyana cewa abin bakin ciki ne yadda Najeriya ke cikin kasashen da talauci ya fi shafa.

Tsohon mataimakin shugaban ya bukaci da a samar da hanyoyin da mutane za su bi wajen kawo karshen talauci, yana mai jaddada cewa dole ne kowane dan Najeriya ya kasance cikin hadin kai.

Ya kuma bayyana talauci a matsayin babban abin da ke haifar da cututtuka, jahilci, da rashin tsaro, inda ya bukaci gwamnatoci, masu ruwa da tsaki, kungiyoyin fararen hula, da su hada hannu wajen yakar annoba talauci ta kowacce fuska a Najeriya.