Gwamnan jihar Kaduna ya Sanata Uba Sani ya kaddamar da rijiyar burtsatse mai amfani da hasken rana a sansanin masu yi wa kasa hidima NYSC da ke Kaduna.

An gina rijiyar ne a dakin kwanan dalibai mata, kuma an aiwatar da shi ne ta hannun hukumar samar da ruwan sha da tsaftar muhalli ta jihar RUWASSA.

An gudanar da bikin kaddamar da rijiyar ne a sansanin masu yi wa kasa hidima a Jihar, inda hakan ya samu gagarumin yabo daga hukumar yi wa kasa hidima NYSC a jihar Kaduna, tare da yabawa gwamna Uba Sani bisa jajircewarsa da kuma irin goyon bayan da yake bai’wa al’ummar jihar.

Da ta ke jawabi a wajen taron Ko’odinetan NYSC a Jihar Misis Efeke Murna Dadaza, ta yaba wa Gwamna Uba Sani bisa yadda ya amsa bukatarsu cikin gaggawa da kuma samar da yanayi mai kyau ga masu yi wa kasa hidima a Kaduna.

Ta yi alkawarin cewa hukumar NYSC za ta tabbatar da kula da rijiyar da kuma amfani da ita yadda ya kamata wajen inganta rayuwar masu yiwa kasa hidima, musamman mata.

Injiniya Mubarak Shehu Ladan darakta Janar na RUWASSA ya bayyana cewa aikin ya yi daidai da aikin hukumar na samar da tsaftataccen ruwan sha mai tsafta a tsakanin mazauna karkara da hukumomi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: