Shugaban jam’iyyar APC na kasa Nentawe Yilwatda ya ce wasu fitattun ‘yan jam’iyyar ADC za su koma jam’iyya APC a mako mai zuwa.

Shugaban jam’iyyar ya bayyana hakan ne a wata ganawa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a garin Jos a jihar Filato, inda ya ce a makonni masu zuwa zai karɓi wasu fitattun ƴan siyasa daga jam’iyyar hadaka ta ADC.
Shugaban ya kara da cewa da yawa daga cikin wadanda suka koma APC sun kammala tantancesu, inda daga bisani kuma za a bayyana su a hukumance a mako mai zuwa.

Yilwatda ya bayyana cewa akwai wasu ‘yan siyasa da suka hada da Sanatoci, gwamnoni, da ‘yan Majalisun dokoki ta kasa da ke shirin komawa jam’iyyar.

Acewarsa jam’iyyar APC na maraba da dukkan wanda ke shirin shiga cikinta kofa a buɗe ta ke.
A makonnin baya-bayan nan dai jam’iyyar APC ta samu sabbin masu shigowa cikinta daga jam’iyyun adawa gabanin babban zabe na 2027.
Ko da a ranar Talata gwamnan jihar Enugu Peter Mbah ya koma jam’iyyar APC daga PDP, yayin da kuma rahotanni ke nuni da cewa gwamna Douye Diri na Bayelsa shima zai bayyana sauya shekarsa nan ba da dadewa ba.