Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Kasa INEC reshen Jihar Anambra ta sanar da shirinta na gudanar da aikin tantance masu kada kuri’a a jihar Anambra domin gwada ingancin tsarin tantance masu kada kuri’a da na’urar BVAS gabanin zaben gwamnan Jihar da za a yi a watan Nuwamba.

Daraktar wayar da kai da wayar da kan masu kada kuri’a Eta-Messi ce ta bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar.

Ta ce za a gudanar da aikin ne a ranar Asabar 25 ga watan Oktoban nan, a wasu fitattun rumfunan zabe na mazabu uku na jihar.

Sanarwar ta bayyana cewa aikin nada nufin tantance lokacin amfani da BVAS da aike da sakamakon zabe a shafin duba sakamakon zaɓe na hukumar gabanin zaben gwamnan.

Sanarwar ta yi kira ga masu kada kuri’a a yankuna da za a gudanar da gwajin, da su bayar da hadin kai yadda ya kamata, inda ta ce zuwan su nada matukar muhimmanci wajen daidaita tsarin gudanar da ayyukan hukumar da fasaha gabanin zaben.

A gefe guda kuma hukumar ta ce za a fara rabon katin zabe na dindindin ga sabbin masu kada kuri’a a jihar daga ranar Laraba 22 ga watan Oktoba.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: