Rundunar ƴan sanda a jihar Benue sun tabbatar da mutuwar wani da a ke zargi da kisan kai a karamar Hukamar Tarka a jihar.

Mai magana na da yawun hukumar DSP Udema Edet ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai yau Litinin a Makurdi.
Edet ya ce wanda ya mutu a na zarginsa da kashe shugaban mafarauta a ƙaramar hukumar Tarka a jihar da a ka kasheshi a ranar 20 ga watan Yuni da ya gabata, sai kuma matarsa da a ka kashe a ranar 11 ga watan Fabrairun shekarar 2023.

A cewar sa duka lamarin ya faru a Wannune, helkwatar ƙaramar hukumar Tarka a jihar.

Kakakin ya ƙara da cewa, bayan samun bayanan sirri a kan wanda a ke zargin a ranar 18 ga watan Oktoba, sun samu labari wanda a ke zargin ya koma Makurdi da nufin kai wani hari
Dalili kenan da ya sa a ka aike da jami’an tsaro tare da kamashi a yankin Geoge Akume Way da ke Makurdi.
Yan sanda sun ce wanda a ke zargin ya buɗewa jami’an wuta sai dai sun mayar da martani wanda har su ka kai ga kamashi.
Daga bisani su ka kaishi asibiti sakamakon rauni da ya samu wanda a nan a ka tabbatar da mutuwarsa.
A cewar sanarwar yan sanda a jihar, sun kwato bindiga kirar AK47 guda ɗaya, da wata bindiga kirar gida sai wasu harsashi masu yawa
Yan sandan sun shawarci jama’a da su bayar da bayanai kan duk wani motsi da ba su gamsu da shi ba a ko ina a faɗin jihar.