Rundunar ƴan sanda a Kaduna sun tabbatar da kashe jami’ansu biyu yayin da a ka kai musu wani hari ofishinsu da ke Zonkwa a ƙaramar hukumar Zangon Kataf a jihar.

Yan bindiga sun kai hari ofishin ƴan sandan ne da ƙarfe 9pm na dare a ranar Juma’a a wani yunƙurin kwatar wasu yan uwansu da a ka kama.

Mai magana da yawun yan sanda a Kaduna Mansir Hassan ne ya tabbatar da haka yau Litinin, ya ce an kashe yan sandansu DSP Monday Madaki da Isfekta Bin Magaji bayan sun ji raunin harbi a jikinsu amma an yi gaggawar kai su asibiti kuma a nan ne likitoci su ka tabbqtar da mutuwarsu.

Sanarwar ta ce ƴan bindiga sun tsere jim kaɗan bayan kai harin gabanin soji da ƴan sanda su kai ɗauki wajen.
A cewarsa ba a sace makami ko guda ba kuma su na ci gaba da aikin farautar waɗanda su ka kai harin.

Sanata mai wakiktar shiyyara Sanata Katung ya buƙaci ƙarin jami’an tsaro a tankin don tabbatar da cewar an kama waɗanda su ka kai harin tare da yi musu hukunci.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: