Kungiyar malaman Jami’o’i ta Ƙasa da Kungiyar Kwadago NLC sun hada kai a yunkurin da suke yi na ganin an magance matsalar da ke faruwa tsakanin ASUU da gwamnati.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da NLC ta bayar da wa’adin makonni hudu ga gwamnati da ta kammala tattaunawa da kungiyoyin ilimi da masu zaman kansu a manyan makarantu.
NLC ta bayyana hakan ne bayan wata ganawa da ta yi da shugabannin kungiyar malaman jami’o’i, manyan ma’aikatan jami’o’in, kungiyar kwalejojin ilimi, kungiyar malaman kwalejin kimiyya da fasaha, manyan ma’aikatan kwalejin kimiyya da fasaha ta Najeriya da sauransu a ranar Litinin, akan yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i ta Kasa ASUU ke yi da sauran matsalolin da ma’aikata a manyan makarantun kasar ke ciki.

An gudanar da taron ne a shalkwatar NLC ta kasa da ke Abuja, domin samar da mafita mai dorewa kan batutuwan da suka biyo bayan gazawar tattaunawar da suka yi da gwamnatin tarayya.

Kungiyar ta NLC ta jaddada cikakken hadin kai da kungiyar ASUU da sauran kungiyoyin ilimi, tare da yin kira ga dukkan shugabannin kungiyar da su bayar da hadin kai.
Da yake karin haske ga manema labarai a karshen taron shugaban kungiyar NLC na kas, Joe Ajaero ya ce sun yanke shawarar bai’wa gwamnatin tarayya wa’adin makonni hudu don kammala duk wata tattaunawa da bangaren.
Ko kuma su dauki matakin da ya dace a kai.
ASUU dai ta fara yajin aikin ne a ranar 13 ga watan Oktoban nan, bayan gazawar gwamnatin na kin magance matsalolinsu.