Asusun ba da lamunin ilimi a Najeriya NELFUND ya bayar da sanarwar bude shafin neman lamuni na dalibai don fara karatun shekarar 2025 da 2026, tare da bayar da damar samun tallafin kudi ga ɗalibai a manyan makarantun kasar.

Asusun ya ce aikin shafin zai fara ne daga ranar Alhamis 23 ga Oktoban nan, zuwa Asabar 31 ga Janairu 2026 mai kamawa.

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da daraktan Sadarwa na NELFUND, Oseyemi Oluwatuyi ya fitar ranar Talata.

Asusun ya yaba da hadin kan manyan makarantun kasar nan, ya kuma bukacesu da su ci gaba da bayar da hadin kai don tabbatar da tsarin lamuni mai inganci ga dukkan daliban da suka cancanta.

NELFUND ta umurci duk manyan makarantun da aka amince da su sabunta da bayar da ingantattun bayanai akan shafin.

NELFUND ya ce sabbin daliban za su iya yin amfani da ko dai ta hanyar amfani da lambar shiga ko kuma lambar rajistar JAMB, yayin da ake karfafa wa makarantun da su nuna sassauci da lokacin rajista da kuma biyan lamunin karatu ga daliban da ke jiran biya.

Sanarwar ta ce makarantun da ba su fara zangon karatun su na 2025 da 2026 ba, da su bayyana da rubuta sanarwa ta musamman ga NELFUND tare da tsarin karatunsu da aka amince da shi don tsarawa.

NELFUND ta kuma yi kira ga dukkan makaratun da su yi duba da matakan rajista na wucin gadi ga daliban da ake aiwatar da aikace-aikacen lamuni don tabbatar da cewa babu wani dalibi da ya rasa damar samun ilimi saboda karancin kudi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: