Majalisar wakilai ta ce za ta gudanar da bincike kan yadda ake amfani da sama da dala biliyan 4.6 na tallafin da Najeriya ta samu don yaki da cuta mai karya garkuwar jiki HIV, tarin fuka, da zazzabin cizon sauro, da kuma karfafa tsarin kiwon lafiyar al’umma.

Matakin ya biyo bayan amincewa da kudirin da mataimakin shugaban majalisar Hon Philip Agbese daga Jihar Benue a jam’iyyar APC a gabatar a ranar Talata.

Da yake gabatar da kudirin mai taken bukatar binciken Tallafin Sama da Dala Biliyan 1.8 da Dala Biliyan 2.8 da Najeriya ta karba daga Asusun duniya da USAID daga shekarar 2021 zuwa 2025, Agbese ya ce Najeriya ta ci gajiyar tallafin da kasashen duniya ke bayarwa, amma sai dai ta ci gaba da samun sakamako mara kyau wajen bayyana sakamako mai kyau ga manyan kalubalen kiwon lafiyar al’umma.

Ya bayyana cewa Najeriya ta samu tallafin dala biliyan 1.8 daga asusun duniya daga shekarar 2021 zuwa 2025 domin yaki da cutar HIV, tarin fuka, da zazzabin cizon sauro, baya ga dala biliyan 2.8 daga hukumar raya kasashe ta Amurka USAID tsakanin shekarar 2022 zuwa 2024 domin magance matsalolin kiwon lafiya.

Agbese ya kuma kara da cewa, kasar ta kuma amfana da tallafin kiwon lafiya na sama da dala biliyan 6 daga shirin gaggawa na shugaban kasar Amurka na yaki da cutar HIV a daidai wannan lokacin domin yaki da cutar da kuma gina karfin al’umma da tsarin kiwon lafiya.

Ya bayyana damuwarsa cewa duk da dimbin jarin da ake zubawa, har yanzu Najeriya na da kaso mai tsoka na cututuka a duniya.

Acewarsa Najeriya ce Kasa ta uku a duniya wajen yawan masu dauke da cutar HIV, kuma ita ce ta fi kowacce yawan masu dauke da cutar a yammacin Afirka da tsakiyar Afirka.

Ya kara da cewa Najeriya ce ta daya a nahiyar Afrika kuma ta shida a duniya a yawan masu fama da cutar tarin fuka, wanda ya kai kashi 4.6 na yawan tarin tarin fuka a duniya, yayin da ita ce tafi kowacce kasa yawan masu dauke da cutar zazzabin cizon sauro a duniya, wanda ya nuna kusan kashi 26.6 cikin 100 na masu kamuwa da cutar a duniya da kuma kashi 31 na mace-macen akan zazzabin cizon sauro.

Dan majalisar ya yi gargadin cewa matukar ba a sauya yanayin ba, Najeriya na fuskantar barazanar gaza cimma burin Majalisar Dinkin Duniya na kawar da cutar HIV, tarin fuka, da zazzabin cizon sauro nan da shekarar 2030.

Da take amincewa da kudirin, majalisar ta umurci kwamitinta mai kula da cutar HIV, tarin fuka da zazzabin cizon sauro da ya binciki yadda aka yi amfani da tallafin da Najeriya ta samu a tsakanin shekarar 2021 zuwa 2025, tare da bayar da rahoto cikin makonni hudu domin ci gaba da aiwatar da dokar.

Haka kuma ta umurci ministan lafiya da ya gabatar da shirin aiwatarwa da duk wani amincewa da majalisar dokokin kasar ta bayar na kashe kudaden.

Leave a Reply

%d bloggers like this: