Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta kama wani matashi mai shekaru 32 Anas Dauda, mazaunin unguwar Jalingo B, a zamabar Lamorde a karamar hukumar Mubi ta Kudu bisa laifin mallakar bindiga ba bisa ka’ida ba.

Kakakin rundunar ‘yan sandan SP Suleiman Nguroje ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a Yola.
Nguroje ya ce kama shi ya biyo bayan yada wani faifan bidiyo da aka yada a kafafen sada zumunta da ke nuna wanda ake zargin yana nuna bindiga kirar AK-47 cike da mujallu uku a lokacin da yake yin sharhi da barazana da kuma takama da cewa zai iya sayar da makaman ko kuma ya hayar da makamin a kan wani adadi na kudi.

Sanarwar ta kara da cewa Bidiyon wanda ya haifar da firgici da fargaba a tsakanin mazauna garin, wanda hakan ya janyo hankalin ƴan sanda.

Da samun rahoton kwamishinan ‘yan sandan Dankombo Morris ya bayar da umarnin aikewa da jami’an ofishin ‘yan sanda na shiyyar Mubi ta Kudu, karkashin jagorancin baturen ‘yan sanda domin ganowa tare da kama wanda ake zargin.
Acewar Nguroje sun yi nasarar bibiyar Dauda tare da kama shi a wani wuri mai nisa a cikin garin Mubi.
Nguroje ya kara da cewa Yayin da ake ci gaba da bincike, ana ci gaba da kokarin kwato haramtattun makaman da aka gani a bidiyon da kuma gano tushen sa.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar ya umurci mataimakin kwamishinan ‘yan sanda mai kula da sashin binciken manyan laifuka na jihar da ya dauki nauyin lamarin domin gudanar da bincike mai zurfi da kuma tuhume-tuhume.
Morris ya kuma baiwa al’umma tabbacin ci gaba da jajircewar rundunar na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi a fadin jihar.
Ya kuma gargadi jama’a da kungiyoyi da su guji shiga ayyukan da za su kawo cikas ga zaman lafiyar jama’a ko kuma karya dokokin kasa.
