Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a birnin tarayya Abuja ta umurci jam’iyyar PDP da ta dakatar da ci gaba da gudanar da shirye-shiryen babban taronta na Ƙasa da ake shirin gudanarwa a garin Ibadan din Jihar Oyo a watan Nuwamba mai kamawa.

Alkalin kotun mai shari’a James Omotosho ne ya bayar da umarni ne a lokacin da yake yanke hukunci a wata kara da aka shigar don tantance cewa ko jam’iyyar za ta iya ci gaba da gudanar da shirye-shiryen babban taronta na kasa da ta shirya gudanarwa a ranakun 15 da 16 ga watan Nuwamba.

Dakatarwar na zuwa ne bayan da Austine Nwachukwu shugaban jam’iyyar a Jihar Imo, da Amah Abraham Nnanna shugaban jam’iyyar A jihar Abia, da kuma Turnah Geoge sakataren jam’iyyar a shiyyar kudu maso Kudu suka shigar da kara.

Wadanda ake tuhuma a cikin karar sun hada da Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa INEC, jam’iyyar PDP, Sakataren Jam’iyyar na kasa Samuel Anyanwu, Sakataren tsare-tsare na Kasa Umar Bature, Kwamitin Ayyuka na Kasa NWC da kuma Kwamitin Zartarwa na Kasa NEC.

Mai shari’a James ya kuma haramtawa hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasa INEC sanya idanu a yayin zaben.

Ana dai kyautata zaton masu shigar da karar nada alaka da ministan babban birnin tarayya Abuja Nyesom Wike, wadanda suka yi kakkausar suka kan taron, tare da bukatar kotun da ta dakatar da taron, su na masu cewa jam’iyyar ta gaza bin kundin tsarin mulkinta, da Kundin tsarin mulki kasa na 1999, da kuma dokar zabe, wajen shirya babban taron.

Sai dai jam’iyyar ta PDP ta ce karar ta shafi harkokinta na cikin gida ne, don haka ta fita daga hurumin kotun,tana mai cewa masu karar na kokarin kawo cikas ga shirye-shiryen gudanar da taron nata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: