Cikin ƙarin muƙarrabai da gwamnan jihar Kano ke yi don riƙe wasu madafu don tabbatar da nasarar gwamnatinsa, Gwaman jihar Kano Abdullahi Ganduje ya sake naɗa Hajiya Fatima Abdullahi Dala a matsayin mai bashi shawara kan walwalar mata ƙananan yara.

Cikin sanarwar da ta fito daga babban sakataren yaɗa labaran gwamnan Kano Mallam Abba Anwar, cikin mutane biyar da aka naɗa akwai Hajiyar Ƴar Dada maikano Bichi a matsayin mai bashi shawara kan ƙungiyoyi masu zaman kansu wadda a baya ta zamto kwamishiyar harkokin mata ta jihar Kano.

Sai Dakta Fauziya Buba a ɓangaren lafiya, daHajiya Aishatu Jafaru mai bashi shawara kan ciyarwar makarantu, sai kuma Hajiya Hama Ali Aware.

Dukkansu gwamnan ya ja hankalinsu da su kasance masu aiki tuƙuru don sauke nauyin da aka ɗora musu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: