Najeriya na Daf da shiga jerin kasashen dake dogaro da kansu wurin noman Shinkafa.

Ministan yada Labarai da Al’adu Alhaji Lai Mohammad ne ya bayyana hakan ga manema Labarai a lokacin da yake bayanin nasarorin da gwamnatin Shugaban kasa Muhammad Buhari ya samo a shekarar da mukayi ban kwana da ita.
Lai Mohammad yayi jawabin ne a jihar legas inda yace tun bayan rufe iyakokin Najeriya aka rage fasa kaurin Shinkafa zuwa kasar nan.

Ya kuma kara da cewa kafin a rufe iyakokin Najeriya manoma Shinkafa basu da yawa amma yanzu yawansu ya kai Miliyan 6 a najeriya.

Haka zalika a baya ana noma Shinkafa ne sau biyu a shekara amma yanzu manoma sau uku suke nomawa a shekara.