An gudanar da taron ne a yau tare da masana a harkar lafiya da shugaban kwamitin kar ta kwana a kan Corona wato mataimakin gwamnan Kano Dakta Nasiru Yusif gawuna.

Cikin samarwar da babban sakataren yaɗa labaran gwamnan Kano mallam Abba Anwar ya fitar ya ce, an gana ne kan yadda za a bi matakan kare kai don gujewa kaamuwa da cutar corona virus.
Duk da kasancewar abin ya shafi dukkan ɓangaren gudanar da rayuwar al umma,amma hakan ne mafita don kaucewa yaɗuwar cutar inji Gawuna.

Cikin hanyoyin da za a bi akwai hana hmgausawa da hannu, bayar da tazara da kuma kaucewa shiga taro.

Shugaban majalisar sarakunan Kano sarkin Kano Aminu Ado Bayero ya bayyana cewar za a bi dukkan hanyoyi wajen wayar da kan al ummar jihar nan ta hanyar Hakimai, Dagatai, masu unguwanni da kuma limamai.
An gudanar da taron a ɗakin taron gwamnatin Kano.