Daga Maryam Muhammmad

Gwamnatin jihar Kano zata duba yiwuwar baiwa masana’antu damar budewa domin gudanar da ayyukansu.

Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje shine yabayyana hakan lokacin daya karbi bakuncin ‘ya’yan kungiyar masu masana’antu ta kasa rashen jihar Kano.

Gwamna Ganduje ya bayyana cewa, gwamnati Zata duba yiwuwar Kara kwana guda a cikin ranakun aiki domin baiwa masana’antun damar gudanar da ayyukansu.

Da yake jawabinsa shugaban kungiyar masu masana’antu ta kasa reshen jihar Kano, Sani Hussaini Saleh, yace Sunzo gidan gwamnatin kano ne domin bayyanawa gwamnati matsalolin da suke fuskanta musamman a wannan hali da ake ciki na zaman gida, inda suke fatan sassauci daga bangaren gwamnati.

Shima anasa bangaren, shugaban cibiyar kasuwanci da masana’antu na jihar Kano Alh Dalhatu Abubakar yace, zasu hada hannu da gwamnati domin kiyaye ka’idojin da aka saka na Kare kai daga kamuwa da cutar Covid 19 da zarar an basu damar bude masana’antunsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: