Rundunar ƴan sandan jihhar Kano ta kama wani Aminu Farawa bisa zargin kulle ɗansa har tsawon shekaru bakwai.

“Tsawon shekaru bakwai babu kulawar lafiya balle abinci” a cewar kakakin rundunar DSP Abdullahi Haruna.

Aminu Farawa mazaunin unguwar Farawa ya kulle ɗansa Ahmed Aminu mai shekaru 30 a duniya a cikin garejin mota.

Bayan samun rahoton hakan rundunar ƴan sanda sun tura dakarunsu na kan kace kwabo waɗanda suka kamo mahafin matashin sannan suka garzaya da matashin asibiti don duba lafiyarsa.

Ko da rundunnar ta tuntuɓi mahaifin dalilin kullen ɗan nasa, mahifin ya ce ya kulle ɗan nasa ne tsawon shekaru uku sakamakon shaye shaye da ya fara.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sanda a Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce tuni kwamishinan ƴan sandan jihar Habu A. Sani ya bada umarnin mayar da ƙorafin zuwa helkwatar rundunar don zurfafa bincik tare da gurfanar da mahaifin a gaban kotu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: