Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace mutane huɗu a garin kankiya ta jihar katsina.

Rundunar ƴan sandan jihar katsina ta tabbatar da faruwar lamarin kamar yadda mai Magana da yawunta SP Gambo Isah ya bayyana.

Gambo Isa yace hukumar yan sanda na iya kokarinta don ganin an ceto mutanen da aka sace.

Ko a ranar litinin din da ta gabata sai da wasu yan bindiga suka yi garkuwa da shugaban ma aikatar lafiya matakin farko a jihar Katsina.

Harin ƴan bindiga na cigaba da ta azzara lamarin da har yanzu aka gaza daƙile ayyukan masu garkuwa da mutane.

Jihohin Katsina, Zamfara da Sokoto na cikin barazana sanadin sace sacen mutane da ya yawaita a wasu yankunan garin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: