Aƙalla mutane 25 ne suka rasa rayukansu sakamakon fashewar tankar mai a jihar Kogi.

Rundunar ƴan sandan jihar ta tabbatar da mutuwar mutanen bayan motar man ta kwace daga hannun direban kuma ta kama da wuta.

Al amarin ya faru a safiyar yau laraba a garin lokoja babban birnin jihar kogi.

An gano wasu ƙananan motoci da suka kama da wuta bayan tankar man ta faɗi.

Wasu da al amarin ya faru a kan idonsu sun bayyana cewar, direban yayi kokarin sanar da mutane motar ta kwace daga hannunsa, amma ba a kulashi ba.

Motar ta kwace daga hannun direban ne a yayin da yake tsaka da tuƙi a kan titi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: