Wasu da ake zargin ƴar ƙungiyar Boko Haram ne sun kaiwa tawagar gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum hari.

Wannan ne karo na biyu da ake kaiwa gwamnan hari kamar yadda a baya gwamnan ya zargi rundunar sojin ƙasar.
Aƙalla jami an tsaro bakwai ne suka rasa rayukansu a yayin harin sai kuma wasu daga cikin ƴan tawagarsa.

Gwamnan ya tafi Munguno a jirgi mai saukar ungulu daga nan ne kuma sai ya nufi baga a ayarin motoci kuma a kan hanyarsu ne lamarin ya faru a yammacin juma’a.

Jihar Borno ta shiga rikicin Boko Haram sama da shekaru goma da suka wuce.