Wasu matasa a jihar Kano sun nuna rashin goyon baya a kan rushes ashen na musamman a rundunar yan sanda don yaƙi da aikata Fashi wanda aka fi sani da SARS.

Matasan sun yi tattaki har bakin helkwatar rundunar yan sandan jihar Kano tare da nuna rashin jin daɗi a bisa yadda aka rushe dakarun.

 

Kamar yadda suka bayyana cewar a jihar Kano jami an na ƙoƙari don ganin an samar da zaman lafiya, kuma ansamu raguwar aikata muggan laifuka a jihar sakamakon ƙoƙarin dakarun SARS.

Jagoran matasan da suka yi tattakin kwamaret Aminu Ahmad Mendieta ya bayyana cewar kawar da dakarun wani koma baya ne a cikin al ummar Najeriya musamman jihar Kano.

Ya ƙara da cewa an samu raguwar ayyukan daba da kwace da fashi da makami a jihar Kano sakamakon sadaukarwar da dakarun suke a wajen aiki a don haka sune nuna ƙin amincewa da wannan tsari na soke ayyukan dakarun.

A nasa bangaren shugaban kwamitin hulɗa day an sanda da jama’a jihar Kano Dakta Sale ya marawa matasan baya a bisa dogaro da kalamansu na cewa dakarun na iya ƙoƙarinsu na ganin an daƙile ayyukan fashi da makami, garkuwa da mutane, da sauran muggan laifuka a jihar Kano.

Ko a jihar Katsina ma haka lamarin yake, said a matasa suka yi tattakin nuna rashin goyon bayan rushe dakarun SARS a Najeriya.

A yau ne dai sufeton ƴan sandan Najeriya Muhammada Adamu ya bayyana dakatar da ashen ƴan sanda na SARS tare da alƙawarin ƙirƙirar sabon sashe da zai cigaba da ayyuka na daƙile fashi da makami a Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: