Connect with us

Labarai

Mun tanadi hanyar hukunta masu saka fim ko waƙa a youtube a wajen Kano – Afakallahu

Published

on

A mu hukunta duk wanda ya saka fim ko waƙa a youtube matuƙar bamu tantance ba ko a wanne gari yake – A cewar Afakallahu

Shugaban hukumar tace fina finai da ɗab i ta jihar Kano ya ce wajibi ne a kai musu duk wani fim ko waƙa su tantance kafin a sakeshi a Youtube.

Afakallahu ya bayyana hakan ne yayin zantawarsa da Mujallar Matashiya a yau Litinin.

Ya ce wajibi ne duk wanda yayi rijista da hukumar ya bi wannan doka ko a wanne gari yake ya bi dukkan dokokin hukumar tace fina finai don tsaftace sana ar.

Sannan kuma ya ce ba iya ƴan jihar Kano dokar ta tsaya ba, ya ce wajibi ne ga duk wani da yayi rijista da hukumar.

Kuma akwai hanyoyin da suka ware don hukunta waɗanda suka saki fim ko waƙa ba tare da an kai sun tace ba.

Guda cikin hanyoyin da za su bi na hukunta waɗanda ba a Kano suke ba shi ne haka kasuwancin fim ko waƙar a yanar gizo a dukkan faɗin jihar.

Afakallahu ya ce manufofi ne masu kyau da hukumar ta tanada don tsaftace masana antar shirya fina finai kuma abin alfahari ne ga jihar Kano kasancewar ita kadai ce ke da tsari a harkar.

Click to comment

Leave a Reply

Labarai

Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 24 A Wani Kauye A Katsina

Published

on

 

Akalla mutane 24 ake zargi an kashe yayin da ƴan bindiga su ka je wasu kauyuka a jihar Katsina.

 

Mafi yawa daga cikin waɗanda aka kashe jami’an sa kai ne na bijilanti da su ka tunkari ƴan bindigan son dakile harinsu.

 

Wani mazaunin garin ya shaidawa gidan talabiji na Channels cewar, a yayin harin wanda aka shafe awanni huɗu a Unguwar Sarkin Noma da ke ƙaramar hukumar Sabuwa a jihar.

 

Ya ce a garin sun shiga ƙauyuka kamar Gangara, Tafi da Kore a daren Alhamis wayewar Lahadi wanda su ka fara harbin iska don tsoratar da mutanen garin.

 

Shugaban ƙaramar hukumar Sabuwa, Faruq Dalhatu ya ce an binne mutane 23 a jiya Juma’a.

 

Ya kara da cewa cikon gawar dayan kuwa na asibiti kuma za a binneshi bayan da likitoci su ka tabbatar da mutuwarsa.

 

Sai dai jami’an yan sanda a jihar ba su ce komai a kai ba.

Continue Reading

Labarai

Gwamnan Katsina Ya Zargi Wasu Daga Cikin Jami’an Tsaro Da Hannu A Ta’addanci

Published

on

Gwamnan jihar Katsina Umaru Dikko Radda ya zargi wasu daga cikin jami’an tsaro da jami’an gwamnati da hannu cikin harkokin ta’addanci a jihar.

 

 

 

Radda ya ce zuwa yanzu an mayar da lamarin kasuwanci.

 

 

 

Ya ce daga cikin waɗanda ke da hannu a ta’addanci a jihar akwa wasu jami’an tsaro da wasu jami’an gwamnati da wasu mutane daban.

 

 

 

Radda ya bayyana haka a jiya Juma’a a tattaunawar da aka yi da shi a gidan talabiji na Channels.

 

 

 

Ya ce harkokin rashin tsaro da ake fuskanta. Ajihar ba gaskiya bane kasuwanci ne wanda wasu jami’an tsaro da na gwamnati ke da hannu a ciki.

 

 

 

Ya ce da yawan matasa a jihar na shiga harkokin ƴan bindiga saboda naira 500.

 

 

 

Ya ce duk da cewar akwai abubuwa da dama da su ke assasawa da kuma bunkasa harkokin ƴan bindiga a jihar da dama amma talauci da rashin adalci na taka rawa matuƙa.

 

 

 

 

Continue Reading

Labarai

Yan Bindiga Sun Hallaka Tare Da Kone Gidajen Unguwa A Kaduna

Published

on

Wasu Yan bindiga sun hallaka mai unguwa tare da kone gidaje a jihar Kaduna

 

 

 

Al’amarin ya faru a ranar Alhamis yayin da su ka far wa ƙauyen Marke a ƙaramar hukumar Makarfi a jihar

 

Dalibi mai sanin makamar aiki Abubakar Ibrahim Shehu na da ci gaban labarin

 

 

 

 

 

 

Continue Reading

Talla

Trending

%d bloggers like this: