Wani matashi mai suna Anas Sa’idu mazaunin garin kwanar ɗan gora a Kano ya buƙaci a ratayeshi a gaban jama’a bayan an kamashi da aikata laifin garkuwa da wani kuma ya hallakashi.

Matashin ya yi garkuwa da shi ne a Hayin Gwarmai ƙarƙashin ƙaramat hukumar Bebeji a Kano.
Rundunar yan sandan jihar Kano ce ta kama matashin bayan mahaifin yaron da aka sace ya kai rahoton abinda ke faruwa.

Matashin Anas ya yi garkuwa da wani mai suna Tijjani mai shekaru 16 kuma ya shaƙeshi har ya mutu sannan ya binneshi a cikin gonarsa.

Alhaji Kabiru mahaifin yaron ya ceɗan garkuwan ya nemi a bashi najira miliyan uku da rabi da katin waya na dubu ashirin kafin ya saki yaron, tun a ranar 9 ga watan Nuwamban da muke ciki ya kai rahoton bayan makwanni biyu kuma aka kama wanda ake zargi.
Mujallar Matashiya ta gano gawar mamacin bayan jami an lafiya sun tabbatar da cewar ya mutu.
Tuni aka miƙa gawar ga iyayen matashin don su sallaceshi.
Duk da cewa matashin ya amsa laifinsa, mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar dacewar sun kammala bincike kuma za su miƙashi a gaban kotu don ya girbi abinda ya shuka.
Sai dai rundunar na jan hankali ga iyaye da su sa ido a kan mutanen da suke mu’amala da su domin mafi yawancin mutanen da ake garkuwa da su makusanta ne ga waɗanda suke ɗaukewa.