Wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun hallaka tsohon sakataren ilimi a jihar Nassarawa.

Ƴan bindigan sun hallakashi a yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Nassarawa.

Lamarin ya faru a Buga wani ƙauye da ke ƙaramar hukumar Toto a jihar, a nan ne ƴan bindigan suka girke manyan itace a kan titi.

Bayan hallaka sakataren ilimin, ƴan bindigan sun yi awon gaba da wasu mutane wanda har yanzu ba a kai ga gano adadinsu ba.

Mai magana da yawun yan sandan jihar Nassarawa ASP Ramhan Nansel ya ce tuni aka aika dakarunsu wajen da abin ya faru, kuma har sun kama wata mota da wayoyi guda biyu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: