Babbar kotun jihar Ekiti ta yanke hukuncin daurin rai da rai ga wani mai suna Samuel Farotimi bayan an sameshi da hada kai da wasu suka yi wa wata fyaɗe.

Alƙalin kotun Adekunle Adeleye ne ya yanke hukuncin bayan an gabatarwa kotu shaidu kuma ta gamsu da shaidun.
Kotun ta samu kwararan shaidu guda biyar wadanda suka tabbatar da faruwar al’amarin .

Samuel ya jagoranci sauran abiokanansa biyu sun yi wa yarinya mai shekaru 14 fyaɗe a ranar 29 ga watan janairun shekarar 2018.

Laifin da aka kama shi da shi kuma ya saɓa da sashe na 516 ma kundin manyan laifuka,. Da kuma sashe na 31 na dokatr kwatowa yara haƙƙin su.
Wadda aka yi wa fyaɗen ta ce mutanen su uku sun tareta a kan hanyarta ta dawo bayan ta siyo gari sannan suka rufe mata baki suka yi mata fyaɗe.
Daga ƙarshe dai jiya Litinin kotun ta yankewa Samuel mai shekaru 27 hukuncin ɗaurin rai da rai a gidan gyaran hali.