Hukumar kare haƙƙin masu siyayya a jihar Kano KSCPC  ta kama wata mota ɗauke da magunguna waɗanda ba su da shaidar hukumar NAFDAC.

An kama motar ne a unguwar Wappa da ke ƙaramar hukumar faggen tsakiyar birnin Kano.

Daga cikin magungunan hukumar ta gano har da maganin ƙarin ƙarfin maza wanda ba shi da shaidar hukumar.

A cikin motar akwai madara da sauran kayan amfani wanda wa’adin su ya ƙare.

Da ma tun a baya shugaban hukumar na riƙo Baffa Babba Ɗan’agundi ya sha alwashin magance masu siyar da kayyakin da suka wuce lokutan su ko kuma na jabu.

Baffa Babba ya bayyana cewar ƙofa a buɗe ta ke ga jama’a domin kai bayanan sirri ga hukumar.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: