Hukumar lafiya matakin farko a Najeriya ta ce an yi wa mutane 513,626 rogakafin allurar korona a fadin ƙasar.

Mutanen da aka yi wa rigakafin sun ƙunshi jihohin ƙasar har da babban birnin tarayya Abuja, sai dai ba a gudanar da ita a jihar Kogi ba.

A rahoton da hukumar lafiya matakin farko a Najeriya ta fitar jiya Lahadi ta ce an yi wa kashi 25.5 ciki ɗari allurar rigakafin.

Ƙasar za ta sakje karɓar kashi na biyu na allurar astra Zeneca wanda aka samar don rage yaduwar cutar Korona.

A cikin jihohin da aka gudanar da rigakafin jihar Legas ke da kaso mafi yawa na mutane 110,042.

Sakamakon zargin da ake na shigar jabun rigakafin allurar Korona zuwa nahiyar Afrika, hukumomi a Najeriya sun ce bas u samu alamu na shigar ta ƙasar ba.

Tuni ƙasashe da dama su ka dakatar da gunar da rigakafin allurar ga ƴan ƙasar saboda zargin illata lafiya a wasu lokutan ma ta kai ga halaka mutane.

Leave a Reply

%d bloggers like this: