Sufeton ƴan sandan Najeriya Muhammad Adamu Abubakar ya umarci kwamishinan ƴan sandan jihar Imo da ya gaggauta kamo ƴan ƙungiyar IPOB da ake zargi da ɓalle gidan yari tare da kai hari helkkwatar ƴan sandan jihar.

A cikin wata sanarwa da mai Magana da yawun ƴan sanda na ƙasa Frmak Mba ya fitar a yau Litinin, yya ce an bayar da umarnin gudanar da bincike a kan hare haren domin gurfanar da waɗanda ake zargi a gaban kotu.
Sannan ya bayar da umarnin zuba jami’an a jihar biyo bayan tagwaye hare-haren biyu da aka kai a tsakanin daren jiya da kuma wayewar yau.

Muhammed Adamu yay i tir da harin da aka kai a jihar wanda ake zargin ƴan ƙungiyar IPOB masu fafutukar ɓallewa daga Najeriya ne su ka kai.

A yayin harin sun kuɓutar da mutanen da aka ajiye a gidan yari a jihar sannan su ka ƙone helkwatar ƴan sanda a jihar.