Gwamnatin jihar Kaduna ta ce ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da kai wa masu garkuwa da mutane magunguna a cikin daji.

Gwamnatin jihar ce ta ce rundunar ƴan sand ace ta kama mutanen biyu a Buruku ƙaramar hukumar Chikun ta jihar.

A cikin wata sanarwa da kwamishinan tsaro a jihar a fitar, y ace an samu rahoton mutuwar mutane uku a ƙasa da awanni 48 a cikin jihar.

Ƴan bindigan sun kashe wani mutum a ƙauyen Rafin Rogo  a ƙaramar hukumar Kajuru ta jihar.

Sai wani hari da ƴan bindiga su ka kai ƙauyen Garu a ƙaramar hukumar Igabi a nan ma su ka kashe mutum guda.

Sannan an kashe wani mutum guda a kusa da maranbar Jos da ke ƙaramar hukumar Igabi a jihar.

Gwamnan jihar ya yabawa jami an ƴan sandan a bisa namijin ƙoƙarin a su ka yin a kama mutane biyu da ake zargi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: