Rundunar ƴan sanda a babban birnin tarayyar Najeriya wato Abuja sun tarwatsa masu zanga-zanga mabiya mazahabar shi’a.

An tarwatsa mabiya shi’a da zu ka fito zanga-zanga ne a Apo-Gudu da ke Abuja.
Mai Magana da yawun yan sandan Abuja ASP Mariam Yusif ce ta bayyana haka a cikin wata sanarwa da ta fitar.

Ta ce mabiya shi’a sun fito zanga-zangar ne a jiya Asabar da nufin tayar da hankalin al’uma.

Sannan babu wanda aka kama daga cikin mutanen da su ka gudanar da zanga-zangar.
ASP Mariam Yusif ta ce rundunar ba za ta zuba ido ana karya doka da od aba, sannan za su yi duk mai yuwuwa wajen
