Rundunar sojin Najeriya ta buƙaci mayaƙan Boko Haram da su miƙa wuya don kawo ƙarshen zub da jini da aka ɗauki lokaci ana yi.

Kwamandan dakarun rundunar Haɗin Kai ɓangare na ɗaya Birgediya Janar A.A. Ryitayo ne ya bayyana haka a yayin wani taron yan jaridu da aka yi jiya a Maiduguri babban birnin jihar Borno.
Rundunar ta buƙaci mayaƙan Boko Haram da su tuba tare da miƙa wuya domin samar da zaman lafiya a jihar.

Rundunar ta tabbatar da cewar a shirye ta ke domin yin afuwa ga mayaƙan Boko Haram da su ka tuba kuma wannan dama a buɗe take a gare su.

Ya ƙara da cewar ba an kai su bane domin kashe mutane saboda kowa ba daɗin hakan ya ke ji ba.
Ya ce wasu daga cikin sun a bibiyar kafafen yaɗa labarai a don haka ya zaɓi yin maganar da yan jaridu domin tabbatar da cewar a shirye rundunar take domin yin afuwa a garesu.
An daɗe ana ɗauki ba ɗadi tsakanin jami’an tsaro da mayaƙan Boko Haram musamman a wasu daga cikin jihohin arewa maso gabashin Najeriya.