Rundunar yan sanda a jihar Ondo ta tabbatar da kama wasu mutane Biyar da ake zargi suna saida sassan jikin mutune.

Ana zargin guda daga cikin su yana haƙo gawa a wata maƙabarta da ke cikin garin Ondo.
Jami’in hulda da jama a na rundunar Tee Leo Ikoro ne bayyana hakan a ranar Alhamis.

Waɗanda ake zargin mutune Biyar sun haɗa da Opeyemi Adetola, Lenre Akintonyo, Clement Adrsanyo, Alowanle Kahinde da kuma Jibiril Jimoh.

An kama waɗanda ake zargin ne a ranar Asabar yayin da guda daga cikinnmasu haƙo gawar ke kan babur ɗauke da wata jaka.
Yayin da ƴan sanda ke bincike a kan abin da ke cikin jakan ne kuma su ka ga sassan jikin mutum a ciki.
Kuma rundunar ta kama sauran mutanen da su ke hulɗar cefanar da sassan jikin mutum.
Sannan ya ce za a ci gaba da bincike daga ƙarshe a tura su gaban kotu domin a yi musu hukunci.