Za’a gina gidajen yarin ne domin rage cunkoso a gidajen yari da su ke Kano da sauran jihohi.

Gwamnatin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ta sha alwashin ƙara gidajen yari a Kano da wasu jihohi.

Ministan harkokin cikin gida Ra’uf Aregbesola ne ya bayyana haka yayin ƙaddamar da helkwatar gidan yari a jihar Osun.

ya ce gwamnatin za ta gina gidajen yari mai ɗaukar mutane 3,000 a tsakanin jihohin Kano, Rives da babban birnin tarayya Abuja.

Wannan wani salo ne da gwamnatin ta ɗauka domin rage cunkoso a gidajen yari na jihohin.

A halin yanzu a na kan gina gidan yari na zamani a Kano da wasu jihohi sannan za a sake gina wasu sababbi a nan gaba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: