Rundunar ƴan sanda a Zamfara ta tabbatar da sace mutane 50 tare da kashe wasu mutne hudu a jihar.

Hakan ya fito daga bakin kakakin ƴan sandan jihar SP Muhammad Shehu a yau Litinin.

Ƴan bindigan sun kai harin ne ƙauyen Goran Namaye a ƙaramar hukumar Maradun ta jihar Zamfara.

Kakakin ya ƙara da cewa ƴan bindigan sun kai harin tare da sace mutanen ne a daren Lahadi.

Sai dai kwamishinan ƴan snadna jihar ya bayar da umarninn ga jami’an sa domin ceto mutanen da aka tafi da su.

Haka kuma an aike da jami’an tsaro yankin da abin ya faru domin samar da tsaro a ɓangaren.

Ko a makon da ya gabata sai da ƴan bindiga su ka kai hari Zamfara tare da sace mutane sama da 60.

Sabon kwamishinan ƴan sandan jihar ya gargaɗi ƴan bindiga a kan su ajiye makaman su ko kuma su ɗauki mataki a kan su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: