Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana farin cikin sa a bisa yadda a ka samu nasarori wajen yaƙi da masu tayar da ƙayar baya a Najeriya.

A yayin da yan jarida ke zanta wa da mai ba shugaban shawara a kan harkokin tsrao Babagana Munguno ya ce shugaban na cike da farin cijin bayan karɓar rahoto a kan yadda ƙasa ke ciki da irin ci gaban da a ka samu wajen yaƙi da ƴan bindiga.

A yau manyan shugabanni a bagaren tsaron Najeriya su ka ziyarci fadar shugaba Buhari domin sanar da shi halin da ake ciki na yaƙi da ƴan ta’addan da su ka addabi Najeriya.

Daga cikin waɗanda su ka kai rahoton akwai ministan tsaro Bashir Magashi mai ritaya, da alƙalin alƙalai na ƙasa da ministan shari’a sai babban harsan sojin Najeriya Janar Lucky Irabo.

Shugaba Buhari y ace zai ci gaba da kawo sauyi wajen yaƙi da ƴan ta’adda musamman a arewa maso gabashin Najeriya.

Tun a watan Agustan da ya gabata shugaban ya ce zai ɗauki matakin da ya dace wwajen yaƙi da masu garkuwa da mutane, ƴan bindiga, da mayaƙan Boko Haram da duk sauran ayyukna ta’addancin da su ka addabi ƙasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: