Wasu da ake zargi ƴan bidniga ne sun kai wani hari a Zamfara ciki har da ofishin ƴan sanda biyu.

Ƴan bindigan sun kwashe makaman jami’an staron su ka yi awon gaba da su bayan sun yi ta harbin iska.
Al’amarin ya faru ranar Alhamis da daddare a garin Shinkafi da ke ƙaramar hukumar Shinkafi a jihar.

Ƴan bindigan sun kai hari wasu wurare da ke garin Shinkafi a ranar Alhamis da daddare.

Sai dai babu cikakken bayanin a kan yadda lamarin ya kasance daga mahukunta kasancewar toshe hanyoyin sadarwar wayar salula a jihar.
Wani mazaunin garin da ya bayyana wa jaridar Daily Trust cewar al’amarin ya faru yayin da mutanen ke sallar Magriba a ranar.
Daga ɓangaren jami’an sanda da ke babban birnin tarayya Abuja ma sun ce ba su da labarin harin da aka kai.
Gwamnatin Zamfara ta toshe hanyoyin sadarwa a jihar domin daƙile ayyukan ƴan bindiga da su ka daɗe su na yi an jihar.
Ko a baya sai da ƴan bindigan su ka kai hari sansanin sojoji tare da kashe wasu duka lokacin da ake tsaka da yaƙi da ƴan bindigan bayan toshe layukan wayar salula a jihar.