Rundunar ƴan sanda a jihar Ogun ta kama wasu masu garkuwa da mutane yayin da su ke ƙoƙarin karɓar kudin fansa.

Al’amarin ya faru a ranar Lahadi kuma an kama mutanen su biyu.
Mai magana da yawun ƴan sandan jihar Abimbol Oyeyemi ya ce masu garkuwan sun sace wani yaro mai shekaru bakwai a garin.

An kama su yayin da su ke ƙoƙarin karɓar kudin fansan yaron bayan sun buƙaci a basu naira miliyan ɗaya.

Bayan kama mutanen da ake zargi an kuɓutar da yarin wanda su ka ɗaure shi a jikin wata bishiya a cikin daji.
Tuni kwamishinan ƴan sandan jihar ya bayar da umar in gudnaar da binciken gaggawa tare da miƙa waɗanda ake zargi a gaban kotu domin fuskantar hukunci.