Rundunar sojin Najeriya na shirin magance matsalar ƴan ta’adda da masu garkuwa d amutane cikin watanni uku.

Rundunar ta ce a cikin watanni uku ta’addanci a Najeriya zai zama tarihi bayan sun samar da wasu runduna guda uku da za su yi yaƙi da ta’addanci.
Rundunar ta samar da wasu dakaru kashi uku waɗanda ake sa ran za a ƙaddamar da su a jihar Enugu.

Babban hafsan sojin Najeriya Janar Farouƙ Yahaya ne zai ƙaddamar da dakarun a jihar Enugu kamar yadda kakakin ya bayyana.

Waɗannan gangami dai za su tinkari dukkan matsalar satar mutane, kashe-kashe da sauran mmiyagun ayyukan da ƙasar ke fuskanta ahalin yanzu.
A na sa ran cikin watanni uku dakarun za su daƙile ayyukan ta’addanciin da ke ciwa ƙasar tuwo a kwarya.
A Najeriya an kasance ana fuskantar hare-haren yan ta’adda a arewa da kudancin ƙasar baki ɗaya.