Mayaƙan Boko Haram a jihar Neja sun shimfiɗa wasu sharuda a yankunan da su ka mamaye.

Mayaƙan sun buƙaci al’ummar wasu ƙauyuka da su janye yaƴan su daga makarantun boko.

Haka kuma mayaƙan sun buƙaci mabiya addinin musulunci da na  kirista da su aurar da yaƴasu mata a yayin da su ka cika shekaru 12 a duniya.

Ƴan Boko Haram sun mamaye wasu ƙauyuka da dama a ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar.

Tun a baya gwamnan jihar ya bayyana cewar mayaƙan na kafa sansani a dazukan jihar kafin daga bisani su fara shiga garuruwa a jihar.

A na zargin mayaƙan Boko Haram na ɓoye a dazukan Kaduna Neja da yayin da ake zargin akwai wasu a jihar Sokoto kamar yadda sanarwar rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewar su su ka kai wa jami’an ta hari a jihar.

a na zargin mayaƙan Boko Haram sun mamaye ƙauyuka da dama a ƙarananan hukumomin Shiroro, Munya, da kuma karamar hukumar Rafi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: