Mayaƙan Boko Haram sun gwabza fada a tsakanin su har aka kashe ƴan ISWAP 87 a yankin tafkin Chadi.

Rahotanni sun nuna cewar an gwabza faɗa a tsakani ne a yankin tafkin Chadi da wani bangare na iaya tsakanin Gwona ta jihar Borno.
Haka kuma an yi fada a cikin wani jirgin ruwa kamar yadda jaridar PRNigeria ta ruwaito.

A tsakanin faɗan da aka gwabza an an kashe mayaƙan su 87 daga ciki an kashe 50 a cikin wani kwale-kwale dai 24 da aka kashe a kan tsaunukan da ke iyakar Mandara da Gwoza.

A na zargin harin da su ka kai wa junan su wata alama ce ta ɗaukar fansa.
Hakan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da samun mayaƙan da dama wadnada ke ajiye makamansu tare da kai kansu ga hukuma.
Hukumomi a jihar Borno sun ce sama da mayaƙan Boko Haram dubu takwas ne su ka ajiye makaman su tare da miƙa wuya.