Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da harin da yan bindiga su ka kai babbar kasuwar Goronyo ta jihar Sokoto.

Muhammadu Buhari ya nuna takaicin a bisa harin da aka kashe mutane masu yawa ranar Lahadi yayin da su ka tsaka da cin kasuwa.

A wata wasiƙa da mai magana da yawunsa Malam Garba Shehu ya fitar, Muhammadu Buhari ya ce kwanaki kadan ya rage wa ƴan bindiga kuma saura ƙiris a kawo ƙarshen su a fadin ƙasar.

Ya ƙara da cewa gwamnatinsa ta ƙara ƙaimi wajen yaƙi da ƴan bindiga waɗanda su ka addabi al’umma a don haka ya buƙaci al’umma su kwanar da hankalin su.

Buhari ya ce rundunar sojin Najeriya na aiki tuƙuru wajen sauya dabarun yaƙi da ƴan bindiga waɗanda su ka addabi ƙasara  ahalin yanzu.

Ya ce a halin yanzu babu wata maɓoya da ƴan bindigan su ke da ita kuma za su kawo ƙarshensu ta hanyar ninka hare-haren da ake kai musu a cikin dazuka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: