“A zangon mulki na farko da Dakta Abdullahi Umar Ganduje, na shekarar 2015 zuwa 2019 an tallafa wa matasa ina jin a miliyan bai fi mutum dubu hamsin ne babu ba kuma a halin yanzu ma ana kan tallafa wa” inji Abba Anwar.

Abba Anwar ya bayyana haka ne jim kaɗan bayan kammala taron cika shekaru biyar da kafa Mujallar Matashiya.

Ya ce ya kamata sauran hukumomi tun daga tarayya har zuwa jiha su shigo domin tallafa wa matasan.

An yi taron cika shekaru 5 da kafuwar Mujallar Matashiya tare da yaye matasa waɗanda su ka koyi sana’o’in dogaro da kai kyauta.

Taron da aka yi a ranar Lahadi wanda ya sami halartar da yawa daga cikin jama’a.

A yayin taron an yi jimamin rasuwar Alhaji Aminu Adamu wanda ake wa laƙabi da Abba Boss a bisa rasuwar sa.

Babban sakataren yada labaran gwamnan Kano Malam Abba Anwar ne ya jagoranci taron da aka yi.

A cikin jawabin sa ya ja hakalin matasa don ganin sun dogara da kan sutare da saka jajircewa bisa tsari da manufa kyakkayawa.

Ya ce hakan zai taimaka wajen sake rage rashin aikin yi da ake fama da shi musamman ganin yadda gwamnatin Kano ke ƙoƙari don ganin an samar da aikin yi a tsakanin matasa.

Abba Anwar ya ce gwamnatin Kano ta tallafawa matasa kusan miliyan ɗaya domin dogaro da kan su a zango na farko na mulkin gwamnan Abdullahi Umar Ganduje.

Wasu daga cikin matasan da su ka amfana daga sana’oin da aka koyar sun yi jawabin godiya.

Taron ya samu halartar wakilcin shugaban hukumar zaɓe ta jihar Kano, manyan ƴan jarida da manyan ƴan kasuwa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: