Bismillahirrahmanirrahim.

Jawabin shugaban Mujallar Matashiya Abubakar Murtala Ibrahim a yayin taron cika shekaru biyar da kafuwar ta ranar 31 Oktoba, 2021.
Godiya ta tabbata ga Allah mai kowa mai komai Allah daya wanda ba a Haifa ba, kuma ba a haifeshi ba sannan ya samar da farko da karshe, Allah ya kara ninka salati ga fiyayyen halitta cikamakin manzanni Muhammadu dan gatan Allah Muhammadu rasululah S.A.W, Allah cikin ikonsa ya nuna mana mana wannan rana mai tarin albarka da kuma dumbin tarihi.

Bayan godiya ga Allah, zan yi amfani da wannan dama domin yin ta’aziyya ga iyalai da yan uwa, abokan arziki da mu kanmu a bisa babban rashi da mu ka yi na uba kuma jigo a Mujallar Matashiya wato Alhaji Muhammad Aminu Adamu wanda ake wa lakabi da Abba Boss.

Hakika Matashiya da al’ummar Kano da ma Najeriya mun yi babban rashi duba ga irin gudunmawar da yake bayarwa a cikin al’umma da dukiyarsa, jikinsa da kuma aikinsa.
A shekarar da ta gabata ya na wannan waje kuma duk wanda ya sanshi ya san irin gudumawar da ya bayar don ganin al’umma ta ci gaba musamman ta hanyar amfani da kafar Matashiya TV don wayar da kai da ilmantar da jama’a.
Mu na sake jaddada addu’a a gareshi da fatan Allah ya ji kan sa ya gafarta masa ya sa aljannar fiddausi ce makoma a gareshi.
A wannan rana da ake cika shekaru biyar da kafuwar Mujallar Matashiya, zan iya bayyana fadi tashi da aka yi a baya wanda mutane daban-daban su ka sadaukar da lokacin su, tunainsu don ganin an samu nasara a kai.
Bayan ganin kokarin da muke yi Allah ya hada mu da wasu mutane masu kishi wadanda ke kai kawo wajen ganin sun tallafe mu da hanyoyin da kudaden shiga za su zo mana domin karfafa gwiwar mu.
A yau an wayi gari Matashiya ta zamto madubin da ake kallo daga da yawa daga cikin yan jaridun da tun kafin a hafeni su ke aiki, amma a yau ita su ke kallo sannan su yi koyi musamman yadda ake kokarin ganin an samarwa al’umma mafita wanda kuma hakan na daga cikin muradinmu.
Cikin ikon Allah da sahalewarsa matashiya ta yi abubuwa da dama tsawon shekarun da aka fara ta, musamman fannin labaran da ke taba mutane na kasa-kasa, da kuma koyar da sana’a ga mutane daban-daban kuma kyauta don su dogara da kansu.
Daga shekarar 2020 zuwa shekarar 2021 da mu ke ciki an kafa tarihi babba wanda tsawon shekarun baya ba mu sami wannan nasara ba, daga cikin nasarorin akwai zakulo labarai na halin rashin ruwa da wasu mutane ke ciki, wanda hakan ya ja hankalin gwamnatin tarayya, gwamnatin jihar, sarakuna, da kungiyoyi attajirai da dama, su ka bayar da gudunmawarsu wanda hakan ya yi silar saukakawa miliyoyin mutane daga halin da su ke ciki a baya.
Hakika wannan nasara ba Matashiya ba ce kadai ta samu, nasara ce da dukkanin masu bayar da gudunmawa da masoya da sauran al’umma wadanda su ka ji dadin hakan.
A cikin wannan shekara guda dai, mun sami nasarar horas da wasu daga cikin yan jarida na jihar Kano da makotan jihar kyauta, a kan muhimman ka’idoji na aikin jarida, da kuma hanyoyin inganta rubutu na Hausa.
Haka zalika cikin huwacewar Allah, mun koyar da matasa sana’o’in daukar hoto mai motsi wato bidiyo, da mara motsi da kuma aikin tantance hoto cikin tsarin kwararru, sannan akwai wasu matasa da mu ka koyawa sana’ar gyaran janareta duka wadannan abubuwa mu na yi ne domin bayar da gudunmawar mu yadda za a rage zaman kasha wando, da kuma saka kishi a zukatan mutane yadda za su dogara da kansu.
Wadannan nasarori ba iyawarmu ba ce mun samu ne daga addu’o’I da kuma kwarin gwiwa da mutane ke bamu sai kuma sakawa a rai cewar kowa na da rawar da zai taka a cikin al’ummar sa.
Sai dai a wannan lokaci da muke kokarin ci gaba da ayyuka irin wadannan, ya na da kyau mutane su ci gaba da karfafarmu ta hanyar ba mu goyon bayan su, wajen siyan hajarmu kamar gurbin talluka da muke da su da kuma bamu ayyuka wanda hakan zai taimaka wajen samar mana da kudaden shiga domin cigaba da samar da nasarori da mu ke sa ran cimma a nan gaba.
Kafin na yi sallama zan mika ta’aziyya ga iyalai iyaye da yan uwa na guda cikin wanda mu ka fara wannan aiki da shi wato Fu’ad Lawal wanda Allah ya yi masa rasuwa, da fatan Allah ya gafarta masa.
Daga karshe ina godiya ga mutanen da su ka halarci wannan waje da ma sauran al’umma baki daya sai godiya ta musamman ga mutanen da ke bamu talluka wanda hakan ke rage mana radadin abubuwan da mu ke kashewa wajen gudanar da ayyuka mu.
Mun gode mun gode mun gode da fatan Allah ya mayar da kowa gidansa lafiya.