Rundunar ƴan sandan jihar Osun ta ce za a duba ƙwƙalwar matar da ta jefa ƴaƴan ta biyu a cikin rijiya ranar Litinin.

Rundunar ta bayar da umarnin duba lafiyar ƙwaƙwalwar matar ne bayan an zarge ta da jefa ƴaƴanta mata biyu a cikin wata rijiya.
Mai Magana da yawun rundunar Yemisi Opalola ta ce gwajin lafiyar ƙwaƙwalwar da za a yi wa matar shi zai ba su damar ɗaukar mataki nag aba.

Ta ƙara d acewa dun da cewar an yi zargin talauci ne ya sa ta aikata hakan amma bas u da wata hujja da za ta tabbatar musu da hakan sai an gwada lafiyar ta.

Opalola ta ce a halin yanzu matar na hannun su kuma kuma za su dauki mataki na gaba bayan an samu rahoto daga likitoci.
Haka kuma ƴaƴan nata biyu da ta jefa a cikin rijiya sun mutu a cewar mai Magana da yawun yan sandan jihar.
An ɗakko gawar yaran mata biyu ne ranar Alhamis bayan an ɗakko wasu ƙwararru da su ka ɗakko su a cikin rijiyar.