Matakin hakan na zuwa ne bayan an tabbatar da ɓullar sabon nau’in Omicron a jikin ƙasar.

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi watsi da haramcin shiga birtaniya ga yan ƙasar ta.
Ministan yaɗa labarai a Najeriya Alhaji Lai Mohammed ne ya sanar da cewar babu hikima a matakin da Burtaniya ta ɗauka na hana yan Najeriya shiga ƙasar.

Matakin hana ƴan Najeriya shiga Burtaniya tna zuwa ne bayan da aka samu rahoton wasu ƴan ƙasar ɗauke da nau’in cutar Korona.

Sai dai gwamnatin ƙasar ta danganta hana ƴan Najeriya da zalunci da kuma horo.
Alhaji Lai Mohammed ya bayyana haka ne a yayin taron ƴan jarida da ya yi yau a Abuja.
Ya ce matakin da Burtaniya ta ɗauka na hana ƴan Najeriya shiga ƙasar ba daidai ba ne duba ga yawan al’ummar da su ke cikin ƙasar.
Kuma gwamnatin ƙasar na iya bakin ƙoƙarin ta don ganin ta kawo ƙarshen annobar Korona musamman sabon nau’in cutar na Omicron.
An samu wasu ƴan Najeriya ɗauke da cutar a bayan sun ziyarci ƙasar Canada sai kuma wasu da aka samu a ƙasar na ɗauke da sabon nau’in cutar.