Guda cikin waɗanda su ka samar da rigakafin allurar Korona ta Astra Zeneca Farfesa Dame Sarah Gilbert ta ce annoba ta gaba ta fi Korona shaɗari.

Farfesa Dame ta ce annobar da ka iya zuwa a nan gaba ta fi ta Korona saurin yaɗuwa sannan ta na da saurin kisa.

Annobar da ake tsammanin za ta iya bayyana a nan gaba na da matukar haɗari kuma ta na da saurin yaɗuwa a cikin jama’a.

Farfesa Sarah ta ce ya kamata a samar da bayanan sirri tare da zuba jari musamman ga masu bincike da kuma kamfanoni domin kare mutane a fadin duniya.

Ta bayar da misali da aikin soja wadda ta ce a kan  tattara bayanan sirri tare da zuba jari don kare hare-hare domin tsare al’umma.

Haka kuma ta shawarci duniya domin ganin an ɗauki matakan kariya daga sabon nau’in Korona na Omicron bayan samun ƙarin bayanai a kan sabon nau’in cutar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: