Baturen zaɓen jihar Imo ya bayyana yadda akayi garkuwa dashi kafin faɗin sakamakon Zaɓen majalisar dattawa.
Jami’in yace an tilastashi ne lallai sai ya bayyana Rochas Okorocha a matsayin wanda ya lashe zaɓen Sanatan.
Jami’in yace yana da buƙatar yaje gida don ya gana da iyalansa don haka ya zame masa wajibi ya faɗi wannan sakamako.
Rochas dai tsohon gwamnan jihar imo ne wanda ya gama wa’adin sa na shekaru takwas yanzu kuma ya fito takarar majalisar dattawa a imo ta tsakiya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: