Rahotanni na nuni da cewar an kama jami’an yan sandan da suka ci zarafin wasu matafiya a wani shingen bin cike a jihar Edo.

Bidiyon cin zarafin da aka dinga yada wa ya tayar da hankula musamman a shafukan sada zumunta.
A cikin faifan bidiyion wani dan sanda ya tare wasu matafiya tare da yi wa wata mata fyade.

Jami’in wanda ke tare da abokan aikin sa shi ma ya harbe wasu mutane kuma an ganshi yana jayayya da wasu matafiya.

Yan Najeriya sun mayar da martani kan yadda ake nuna cin zarafi tare da yin kira da hukumomi su sa baki domin gano bakin zaren.
Rundunar yan sandan jihar ta ce an kama waɗanda ake zargi kuma an fara gudanar da bincike a kan su.
Kwamishinan yan sandan jihar ya ce an kama wannan jami’in da dukkan tawagar sa kuma a halin yanzu suna tsare a hannun yan sanda na jihar Edo.