Ƴan jaridu suna tsaka da aikinsu na ɗaukar rahoto adaidai lokacin da ƴan ƙasar Algeria ke gudanar da zanga zangar ƙin goyon bayan Prime ministan ƙasar Abdulaziz Bouteflika.
Adai lokacin ƴan sanda suka yi awon gaba da wasu ƴan jaridu kimanin 12 sha biyu daga kafafen yaɗa labarai daban daban.

Anan suma ƴan jaridu suka shiga zanga zangar sai an sako musu abokan aikin su.
Sai dai daga bisani wani jami’in ƴan sanda ya bayyana cewa an saki ƴan jaridun.

Zanga zangar da alummar ƙasar algeriya suke yi ya biyo bayan ƙin amincewa da prime ministan ya cigaba da gudanar da mulkin ƙasar wanda ya shafe shekaru akan milki. A yanzu haka yana shekara 81 kuma yana fama da cutar mutuwar ɓarin jiki wanda a yanzu haka baya iya tafiya amma yana neman wa’adin cigaba da mulki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: