Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nuna rashin jin daɗinsa a bisa wahalar man fetur da wutar lanarki da ake fama da ita a Najeriya.

Shugaban ya mika sak=ƙon haƙuri gaƴan ƙasar wanda ya ce sam ba ya jin daɗin halin da ƴan ƙsar ke ciki na wahalar samun wutar lantarki da man fetur.
A wata sanarwa da shugaban ya wallafa a shafinsa na Faecbook, ya ce gwamnatin sa ta yi ƙoƙarin kawar da matsalar man fetur da wutar lantarki a shekaru bakwai da su ka kwashe su na mulkin ƙasar.

Shugaban ya tabbatar da cewar gwamnatin sa na aiki tukuru domin ganin an kawo ƙarshen matsalar sinadarar biyu da ake fama da ƙarancinsu a halin yanzu.

Haka kuma su na aiki da ƙungiyoyin da alhakin hakan ya shafa domin ganin an magance matsalar yadda ƴan ƙsa za su dinga samun wutar lantarki da man fetur ba tare da sun sha wahala ba.
Sannan shugabban ya bayar da umarni ga hukumomi domin ɗaukar mataki ga duk masu hannu wajen kawo wahalar man fetur da ake fama da shi a fadin ƙasar.
A wannan lokaci ƴan Najeriya na ci gaba da fama wajen samun man fetur da kuma ƙarancin wutar lantarki, wanda hakan ya yi silar ƙara farashin kayayyaki a wasu sassan ƙasar.