A wani labarin kuma wasu da ake kyauta zaton ƴan bindiga ne sun abka ƙauyukan Juyi da Doruwa a ƙaramar hukumar Bungudu da jihar Zamfara sannan su ka hallaka mutane 17.

A wata sanarwa da mai bai wa gwamnan jihar shawara a kan kafafen yaɗa labarai Zailani Baffa ya sanyawa hannu, sanarwar ta ce ƴan bindiga sun sace mutane 62 tare da kashe mutane 37 a ƙananan hukumomin Bunguɗu da Bukkuyum na jihar Zamfara.
Sanarwar da aka fitar a madadin gwamnan jihar kuma ya aike da saƙon ta’aziyyar sa ga iyalan waɗanda su ka rasa ƴan uwansu.

Gwamnan jihar ya bai wa hukumar jin ƙai da bayar da tallafi a jihar umarnin kula da mutanen da abin ya shafa domin rage musu raɗaɗin harin da aka kai musu.

Gwamnatin jihar ta ce ba za ta kayara a kan hare-haren yan bindiga ba kuma hakan ba zai sa ta sassauta a ka mataka da ta ke ɗauka na kawo ƙarshen hakan ba.
Jihar Zamfara ta yi ƙaurin suna wajen fuskantar hare-haren yan bindiga wanda hakan ke silar salwantar da rayuwan mutane masu yawa tare da raba dubbai daga muhallinsu.